1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soja za su daura damarar yaki a Somaliya

Yusuf Bala Nayaya
October 22, 2017

Mai magana da yawun sojan kasar dai ya ce za su yi aiki tukuru wajen ganin sun fatattaki mayakan na al-Shabab a wajen da suka fi karfi a kasar da ke a Gabashin Afirka.

https://p.dw.com/p/2mJDz
Bildergalerie Grün in Afrika
Hoto: AFP/Getty Images

Shugaban kasar Somaliya ya yi kira ga dakarun sojan kasar da su shirya damara ta yaki da mayakan al-Shabab wadanda ake zargi da hannu a harin bam da ya yi sanadi na rayukan mutane 350 baya ga raunata wasu 500 a birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar. A kwai dai har kawo yanzu gwammai wadanda suka bace bayan wannan mummunan hari da kasar ta gani a bayan nan.

Shugaba  Mohamed Abdullahi Mohamed ya yi jawabin nasa ne gaban dakarun sojan kasar da dama a sansaninsu da ke kusa da babban birnin kasar a daidai lokacin da kuma wasu ke ci gaba da aiki na kwashe baraguzai na gine-gine da aka yi fata-fata da su a sakamakon harin, suna lalube na sauran jikkuna al'umma.

Mai magana da yawun sojan kasar dai ya ce za su yi aiki tukuru wajen ganin sun fatattaki mayakan na al-Shabab a wajen da suka fi karfi a kasar da ke a Gabashin Afirka. Ana sa ran dai Amirka za ta taka rawa a kokarin da dakarun za su sanya gaba wajen korar mayakan sakan.