Slovenia ta ƙarbi jagorancin Ƙungiyyar Eu
January 1, 2008Talla
Ƙasar Slovenia ta ƙarbi jagorancin Ƙungiyyar Tarayyar Turai Eu, a safiyar yau talata. Batun makomar yankin Kosovo da kuma kundin tsarin mulƙin ƙungiyyar, abubuwa ne da za su kasance ja- gaba, a lokacin wannan jagoranci. Slovenia ta ƙarbi jagorancin ne na tsawon watanni shida daga ƙasar Portugal. Ana sa ran Slovenia za ta miƙa ragamar ƙungiyyar ga Faransa, a ranar ɗaya ga watan yulin wannan shekara. A waje ɗaya kuma ƙasashen Cyprus da Malta, sun shiga cikin da´irar ƙasashe dake amfani da kuɗin Yuro.