Siyasar Turkiyya | Labarai | DW | 10.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siyasar Turkiyya

Yan majalisar dokokin kasar Turkiyya sun koma zama zagaye na karshe ,adangane da mahawara kann kada kuriar raba gardama dangane da gyaran kundun tsarin mulkin kasar,da suka hadar da zaben shugaban kasa,domin kawo karshen rikicin da kasar ke fama dashi dangane da wanda zai zama shugaban kasar na gaba.Gwamnatin kasar ta turkiyya ta dage zaman mahawara kann gyaran kundun tsarin mulkin ne,sakamakon kauracewa zaben da yan adawa sukayi.Yan adawan dai na ganin cewa zabin dan jamiiyyar dake mulki a halin yanzu,zai shafi harkokin siya da rayuwa a turkiyya.