1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Rasha

Abdullahi Maidawa KurgwiDecember 12, 2007

Makomar shugaba Vladimir Putin

https://p.dw.com/p/Cam1
Shugaban Rasha Vladimir PutinHoto: AP

Kafin wannan lokaci al’ummar Rasha sun kasance cikin zullumi da tunani wanda Putin zai zaba don ya gaje shi a wannan kujera ta shugaban kasar Rasha.

Koda shi kansa Dmitry Medvedev, bai kwana da tunani kan cewar shine zai hau wannan kujera ba na shugabanci, wata kila wannan dalili na rashin tabbas ya sanya yan siyasar Rasha ke sanyi sanyi da fitowa fili wajen neman mukamin shugaban kasa a lokacin babban zaɓen kasar da za’ayi cikin watan Maris mai zuwa.

Tun bayan da jama’iyyar dake kan mulki ta (U.R.P) ta lashe zaben yan majalisar dokokin rasha cikin watan jiya,harkokin siyasar kasar Rasha suka soma zamantowa masu harshe guda.

Masu lura da harkokin siyasar kasar sun soma tsokaci cewar da alamu Putin zai mika shugabanci da hanun dama ya karɓe ada hanun hagu, sakamakon yadda ya nuna sha’awar sa ta cigaba da sa hanu a harkokin shugabancin kasar.

Fadar gwamnatin kasar Amurka da ake zato ko zata sa baki cikin wannan sabon tsari na shugabanci a Rasha taƙi tace komai dangane da wannan lamari, to amma an saurara ta bakin wata jami’ar gwamnatin Amurka, Dana Perino, tana cewar Amuirka zata cigaba da gudanar da harkoki na dangartaka da Rasha, koma ba zata tsoma baki ba cikin harkokin siyasar kasar, mussaman wannan sabon yanayi da aka ɓullo dashi .

Yanzu dai abinda duniya ke jira ta gani shine ko wata ƙila shugaba Putin zai sanar da kudirin sa na kasancewa sabon Firaministan ƙasar kafin ranar biyu, ga watan Maris na shekara mai zuwa, ranar da ake zato cewar wa’adin shugaba Putin zai ƙare a mukamin shugaban ƙasa a wa’adin mulkin da yake karo na biyu.

A yau Laraba ake sa rai cewar shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin zai sanar wa al’ummar ƙasar aniyar sa ta riƙe muƙamin Firamnistan Rasha, bayan sanarwar da ya bada na Mr. Dmitry Medvedev matsayin wanda zai gaje shi a muƙamin shugaban ƙasa.