1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasa a Kwango da Habasha sun dauki hankalin jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
January 5, 2018

Majami'ar Katholika ta shiga jerin masu kalubalantar Kabila a Kwango. Firaministan kasar Habasha ya yi alkawarin sako firsinonin Siyasa.

https://p.dw.com/p/2qONh
Unruhen im Kongo
Hoto: Getty Images/AFP/J. Wessels

A wannan makon za mu fara sharhi da labaran jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango tana mai cewa.

Cocin Katholika da ke da angizo a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ya yi kira da a gudanar zanga-zangar neman mulki na demokradiyya bayan an cika shekara guda da majami'ar ta Katholika ta shiga tsakani aka yi sulhu tsakanin gwamnatin Shugaba Joseph Kabila da 'yan adawa kan shirya zabe ckin shekara guda, amma shugaban bai cika alkawari ba. Hukumomi sun haramta zanga-zangar da a karshe aka samu rasa rayukan mutane takwas. Jaridar ta ce umarnin da cocin ya ba wa masu zanga-zangar a bayyane yake, an hana su kone tayoyi da kafa shingaye da tashin hankali da furta kalaman batanci da jifa da dutwatsu da kuma lalata kadarori. An kuma shawarce su da kada su gudu ko mayar da martani ko da sojoji da 'yan sanda sun far musu. Kar su rike tuta ko alamar wata jam'iyya, kowa ya dauki katin shaidar zama dan kasa. Wannan sabon matakin da cocin ya dauka na nuna cewa yanzu cocin na sahun gaba a yekuwar adawa da Shugaba Kabila.

Wasu a harabar Cocin Katholika a Kinshasa
Wasu a harabar Cocin Katholika a KinshasaHoto: Getty Images/AFP/J. Wessels

Kasar Habasha wato Ethiopia za ta sako dukkan fursinonin siyasa inji jaridar Süddeutsche Zeitung inda ta kara da cewa jagoran gwamnatin mulkin kama karya, Firaminista Hailemarie Desalegn mai shekaru 52 ya kuma ba da sanarwar rufe daya daga cikin gidajen firsina na gwale-gwale a kasar.

Shi dai Firaministan ya yi alkawarin fadada abin da ya kira mulkin demokradiyya ga kowa da kowa. Jaridar ta ce wannan matakin da gwamnatin mulkin kama karya ta Habasha ta dauka na zama a karon farko ta amsa cewa lalle akwai firsinonin siyasa a kasar. Sai dai ba a san yawansu, amma kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi kiyasin cewa an kame dubu gommai na mutane musamman tun bayan fara boren kin jinin gwamnati a shekarar 2015. Tun ba yau ba gwamnati ke daukar matakan ba sani ba sabo kan 'yan adawa da 'yan jarida masu sukar lamirinta, inda ma ya kai ta da farfado da dokar yaki da ta'addanci.

Firaministan kasar Habasha
Firaministan kasar HabashaHoto: picture alliance/AA/E. Hamid

Daga batun sakin fursinonin siyasa a Habasha sai na kamfar ruwa a birnin Cape Town da ke zama cibiyar 'yan yawon bude ido a kasar Afirka ta Kudu.

A labarin da ta buga game da karancin ruwa jaridar Berliner Zeitung ta ce tsawon watanni ke nan da aka ayyana dokar ta baci dangane da kamfar ruwa a birnin na Cape Town inda aka rage yawan ruwan da mazauna birnin ke amfani da shi a kowace rana da misali kashi 60 cikin 100.

Su kuma baki 'yan yawon bude ido tun a filin jirgin sama ake tarbarsu da kwalaye masu rubutun a takaita yawan ruwan da ake amfani da shi. Jaridar ta ce duba da halin da ake ciki matukar mahukunta ba su gaggauta nemo bakin zaren magance matsalar ba, to za a shiga mawuyacin hali kafin tsakiyar wannan shekara ta 2018.