Siyasar kasar Iraki | Labarai | DW | 20.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siyasar kasar Iraki

Shugaban Iraqi Jalal Talabani ya ce a shirye ya ke ya gana ido da ido da masu ta da kayar baya dake adawa da gwamnatinsa, idan suna son su tuntube shi. Talabani ya fadi haka ne a gun taron sasanta al´umar Iraqi da kungiyar kasashen Larabawa ta shirya a Alkahira babban birnin kasar Masar. Shugaban ya ce idan wadanda ke kira kansu ´yan tawaye a Iraqi suka nuna sha´awar tattaunawa da shi to zai yi lale maraba da su. Yace ko da yake zai so ya tattauna da duk dan Iraqi amma hakan baya nufin zai amince da dukkan abubuwan da zasu fadi. Taron na yini 3 ya na samun halarcin shugabannin siyasa da na addinai na Iraqi.