Siyasar kasar Iraki | Labarai | DW | 21.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siyasar kasar Iraki

Yayin da jam´iyun siyasa a Iraqi ke shirin yin shawarari masu tsaruri akan kafa wata sabuwar gwamnatin kawance, shugaba Jalal Talabani da shugaban yankin Kuradawa Massud Barzani sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar wadda zata share hanyar kafa wata gwamnati daya tilo da zata ja ragamar mulki a arewacin kasar mai ´yancin cin gashin kai. Kawo yanzu jam´iyar Barzani ta Kurdish democratic Party ke da alhakin tafiyar da harkokin mulki a yankunan Arbil da Dohuk yayin da jam´iyar Patriotic Union of Kurdistan ta Talabani ke iko a lardin Sulaimaniya. To sai dai duk da haka yarjejeniyar ba ta hade jam´iyun guda biyu ba. Jakadan Amirka a Bagadaza Zalmay Khalilzad na daga cikin jami´an diplomasiya da suka halarci zaman majalisar dokokin yankin na Kuradawa.