1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Siyasar Irak da Turkiyya

Rikicin kutsawan dakarun Turkiyya zuwa kudancin Iraki

default

Jiragen Dakarun Turkiyya a arewacin Iraki

To yanzu dai kasashe dabam dabam suna kara nuna fushin su a game da kutsa kan da sojoji da jiragen saman yakin Turkiya suka yi a Irak. Fushin musamman yafi tsanani ne a yankunan Kurdistan na IRak. Gwamnatin wannan yanki ta nuna da cewarf ko da shike tana bukatar kyakkyawar dangantaka da takwatan ta, amma bata son matsalolin da bai shafi Kurdawan Irak ba su shafi mazauna wannan yanki. Ministan harkokin wajen wannan yanki mai cin gashin kansa, a arewacin Irak, Mustafa Bakar yace: Muna sa ran gwmanatin tsakiya a Bagadaza zata fitar da kalmomi masu tsanani na kalubalantar wnanan hali da ake ciki, kuma muna daukar cewar Amerika ita ce take da alhakin wnanan hali da ake ciki. To amma gwamnatin ta tsakiya a Bagadaza, wadda angizon ta kalilan mne kan Kurdfawa dake arewacin kasar, bata fito fili da zuciya daya, ta dauki wnai mataki a game da hare-haren na Turkiya a cikin kasar ta Irak ba. A bayan da tasha nuna cewar hare-haren na Turkiya ba wani abin da za'a damu dashi bane, a yanzu gwamnatin ta Bagadaza ta yarda da gaskiyar cewar aiyukan sojojin na Turkiya a arewacin Irak yana iya wuce gona da iri, musamman idan jamiu'An tsaron Irak da hadin gwiwar Kurdawa a yankin Peshmerga suka shiga dauki ba dadi da sojojion na Turkiya. Idan har aka kai ga wnanana dauki ba dadi, hakan yana iya haifar da mummunan sakamako, kamar yadda ita kanta Amerika ta nunar, musamman ganin cewar duka bangarorin biyu, wato Turkiya da Kurdawan Iraki kawayen ta ne na kusa. Amerika ita ce a shekara ta 1991 ta taimakawa Kurdawan na arewacin Irak suka sami yancin cin gashin kansu daga Saddam Hussein. Hakan ya sanya ministan harkokin weajen Iraki, Hoshiyar Zebari ya gabatar da sanarwa mai karfi a game da halin da ake ciki a yankin na arewacin kasar sa. Kutsawar da Turkiya tayi ta kasa da ta jiragen saman yaki, mataki ne da ya haddasa kara lalacewar halin da ake ciki a yankin, kuma matzaki ne da ke haddasa matukar damuwa da haddasa rashin zaman lafiya. Gwamnatin mu tayi kira ga Turkiya ta kawo karshen wannan mataki nata cikin gaggawa ta janye sojojin ta daga kasar mu. Tsawon watanni biyu kenan muna ganin yadda ake keta mutunci da kin mutunta yancin iyakokin Iraki. Hare-haren sojojin kasa na Turikiya a yanzu mataki ne dake kara hura wutar wannan rikici. Rundunar sojan Turkiya a halin da ake ciki tace yawan mayakan kungiyar PKK da ta kashe sun kai fiye da dari, yayin da sojojin kasar goma sha biyar suka mutu. Sai dai ministan harkokin wajen gwmanatin Kurdawan arewacin Irak, Mustafa Bakar yace a wnanan karo ma, Turkiya ba zata smai nasarar hare-haren nata ba. Yace Turkiya tsawon shekaru ashirin da hudu tana amfani da karfin soja a kan Kurdawa, amma har yanzu bata cimma burin ta ba, wane dalili zai sanya ta cimma burin nata a yanzu.