SIYASAR DAKE AKWAI GAME DA KUNDIN TSARIN MULKIN KUNGIYYAR EU. | Siyasa | DW | 22.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SIYASAR DAKE AKWAI GAME DA KUNDIN TSARIN MULKIN KUNGIYYAR EU.

FARAMINISTA TONY BLAIR NA BIRITANIYA LOKACIN DA YAKE GANAWA DA YAN JARIDU JIM KADAN BAYAN KAMMALA TARON KUNGIYYAR EU A BRUSSELS.

default

A yayin da shugabannin kasashen nahiyar Turai suka amince rabi da rabi game da tsarin kundin mulkin kungiyyar Eu,a yanzu kuma abin da yafi daukar hankali shine na yadda shugabannin zasu jawo hankalin jama,arsu na yarda da abubuwan dake kunshe a cikin daftarin kundin tsarin mulkin don fara amfani dashi a shekara ta 2007 mai zuwa idan allah ya kaimu.

Ba a da bayan wan nan kuma akwai batun zabar shugaban hukumar zartarwa na kungiyyar da zai maye gurbin Mr Romano Prodi da wa,adin sa yake kann karewa nan bada dadewa ba.

A cewar tsohon shugaban kasar Faransa Valery Giscard, babu shakka kundin tsarin mulkin kungiyyar na Eu abune da idan an bishi yadda aka tsara shi ka iya taimakawa wajen ci gaban kasashen dake cikin kungiyyar ta Eu yadda ya kamata.

Babban abu da shugabannin kungiyyar na Eu zasu fi mayar da hankali a kai yanzu a cewar Mr Giscard shine na ganin kundin tsarin mulkin ya samu karbuwa ga alummar nahiyar turai da kuma gudanar da dokokin dake cikin sa yadda ya kamata.

Rahotanni dai sun nunar da cewa Mr Valery Giscard ya fadi hakan ne bisa la,akari da irin rashin fitowar jama,a yadda ya kamata a lokacin gudanar da zabe na yan majalisun dokoki na kungiyyar ta Eu da aka gabatar makonni biyu da suka gabata a hannu daya kuma tare da zulumi da mkuma zaman dar dar da mutane a nahiyar ke ciki na irin gwauron tashin da takardar kudin yuro keyi a halin yanzu.

Tsohon shugaban kasar ta Faransa wanda a baya ya taba shugabantar kwamitin kalailaice wan nan kundin dokoki na kungiyyar ta Eu da aka yarda dashi ya tabbatar da cewa babu ko ja akwai bayanai dake nuni da cewa da yawa daga cikin mutanen nahiyar ta turai na nuna halin ko oho game da abubuwan dake faruwa game da kungiyyar ta Eu a halin yanzu.

A karshe tsohon shugaban kasar na Faransa ya gargadi shugabannin na Eu dasu lura wajen sake gudanar da zabe game da amincewa ko kuma akasin hakan game da abubuwan dake cikin kundin tsarin mulkin kungiyyar na Eu da za a sakeyi a nan gaba a majalisar dokokin kungiyyar ta Eu.

A yanzu haka dai rahotanni sun tabbatar da cewa babban kalubalen dake gaba shine na yadda za a aiwatar da dokokin dake cikin kundin tsarin mulkin kungiyyar,musanmamma bisa laakari da cewa wasu kasashen basu amunta dari bisa dari da abubuwan dake cikin kundin tsarin mulkin kungiyyar ba.

Faraministan Biritaniya Tony Blair yace nan gaba kadan gwamnatin sa zata gudanar da zaben jin raayi na alummar kasar game da dokokin dake cikin kundin tsarin mulkin kungiyyar na Eu.

Bugu da kari kasashe irin su Denmark da Ireland da Portugal da Holland da Belgium ma sun nuna alamun gudanar da zabe irin makamancin wanda kasar ta Biritaniya zata gudanar game da kundin tsarin mulkin kungiyyar na Eu.

Babu shakka matukar mutanen wadan nan kasashe suka amince da wan nan kundi to babu makawa za a aiwatar dashi yadda ya kamata a wani lokaci cikin shekara ta 2007 mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Ibrahim Sani.