1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar ƙasar Gini

September 15, 2010

Sojoji a ƙasar Gini Konakry sun kawar da shakkun da ake yi, kan ko za su yi biyayya ga gwamnatin farar hula bayan zaɓen ƙasar.

https://p.dw.com/p/PCr4
Sekouba Konate, kewaye da askarawansaHoto: AP

Shugaban sojojin ƙasar Gini Konakry dake riƙe da iko a ƙasar, ya jaddada cewa sojojin ƙasar za su yi biyayya ga duk wanda ya lashe zaɓen ƙasar da zai gudana ran lahdi mai zuwa. Da yake jawabi wa sojojin ƙasar a wani bariki dake babban birnin ƙasar Konakry a yau laraba, bayan tarzumar da ta ɓarke a ƙarshen mako, Janaral Sekouba Konate yace aikin sojojin shine kare ƙasar da kuma fararen hula. Bayan da tarzuma ta ɓarke tsakanin 'yan bangan siyasa na ɓangaren Cellou Dalein Jallo da na Alhpa Conde waɗanda za su fafata a zaɓen zagaye na biyu, gwamnatin ƙasar ta haramta duk wani gangamin siyasa da ma yaƙin neman zaɓe. Shi dai jagoran sojojin Sekouba Konate yace sojojin ƙasar basu da wata manufa ta kawo banbancin ƙabila.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu