SIYASA DA RIKICIN IRAKI. | Siyasa | DW | 25.11.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SIYASA DA RIKICIN IRAKI.

Jammiyar yan darikar Sunni dake kasar Iraki,tayi barazanar yin wasti da shiga zaben farko na kasar idan har aka gudanar dashi a ranar 30 ga watan janairu,kamar yxadda aka tsara.

IRAKI.

IRAKI.

Shugaban Jammiyar Mohsen Abdul Hamid ya fadawa kamfanin dillancin labaru na reuters cewa,kamata yayi a dage zaben da watanni 6,saboda hali na rashin tsaro da kasar ke ciki a yanzu haka,idan kuwa ba haka ba zasu janye.

Sai dai gwamnatin rikon kwaryan Irakin da jammiyar yan darikar Shia,wadanda ke rinjayen kashi 60 daga cikin dari na alummar kasar,wadanda kuma ke hangen nasara a zaben,sun lashi takobin cewa sai wannan zabe ya gudana ranar 30 ga watan Janairu ,kamar yadda Mdd ta tsara.

To saidai acigaba da dauki ba dadin da kasar ke fuskanta,an samu karuwan kai hare haren sojojin yakin sunkuru a garin Ramadi dake yammacin Irakin,sakamakon diran mikiya da sojojin Amurka sukayiwa yan sari ka noken garin Falluja,dake makwabtaka da iata.Mai magana da dakarun amurka dake Ramadi ya bayyana cewa yan yakin sari ka noken sun tsere ne daga Falluja sakamakon kasancewar dakarun amurkan a can,ruwa garin na ramadi.

Wannan gari dake zama babban birnin gunduwar Al-Anbar,mai tazarar km 100 yammacin Bagadaza,kana km 50 daga Falluja,na fuskantar hare hare tun daga ranar 8 ga wannan wata da muke ciki.

Sanarwa da dakarun Amurkan suka gabatar a jiya, na bayanin cewa sunyiwa garin Falluja zobe ne domin hana yan yakin sunkurun daga ficewa,amma duk da haka wasu sun samu tserewa zuwa garuruwa dake makwabta.

Acan birnin Bagadaza kuwa an samu fashewan wani abu mai kama da Bomb ,wanda hayakinsa ya turnike sararin samaniya a yankin Green zone dake dauke da gidajen maaikatan ofisoshin jakadancin Amurka da Britania da jamian gwamnatin rikon kwaryan Iraki.Koda yake ya zuwa yanzu babu wata sanarwa dangane da wannan harin daga bangaren sojin Amurkan,ana dai yawan kai hare haren rokoki dana kunar bakin wake da mota a kusa da wannan yankin.

A birnin Basra dake kudancin Irakin kuwa,yan sanda sun sanar da cafke yan yakin sari ka noken kasashen waje guda 5,wadanda suka tsere daga fadan falluja.Bakin dai sun hadar da yan saudiyya 2,da yan tunisia 2 da kuma dan kasar Libya,wadanda ake zargi da ayyukan taaddanci a garin Falluja da kuma tsakiyar Irakin,ata bakin commandan rundunar yansandan Basra Mohammed Kadhem al-Ali.

Baya ga wannan adadin akwai wasu mutane kimanin 40 dake tsare a yanzu haka,wadanda suka fito daga kasashen Yemen,Saudi Arabia,Libya,Syria,Afganistan da nahiyar Afrika.

A yan makonni da suka gabata dai dakarun mamayen sun sanar da cewa zasu kwato dukkan garuruwan dake hannun yan tawaye a Irakin,domin sune ke barazana wa shirin zaben kasar.Yanzu haka dai garuruwan yan Darikar Sunni na Samarra da fallujah na hannun sojin mamayen,inda ahalin yanzu sojin Amurka,Britania dana Irakin suka doshi yankin kudancin Bagadaza.

 • Kwanan wata 25.11.2004
 • Mawallafi Zainab Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveP
 • Kwanan wata 25.11.2004
 • Mawallafi Zainab Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveP