SIYASA A KASAR KENYA | Siyasa | DW | 31.12.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SIYASA A KASAR KENYA

Kwanaki kadan bayan samun nasarar Mwai Kibaki a zaben shugaban kasar kenya,mutanen kasar suka cika da doki na hasashen cewa jim kadan bayan darewar gwamnatin ta Kibaki komai zai canja dangane da kyautata aikin gwamnati tare da gudanar da aiyuka da zasu kyautatawa alummar kasa.

A kuwa ta hasashen talakawan kasar gani suke bayan karshe da gwamnatin ta Kibaki zata kawo na mulkin murdiya da kuma danniya na tsawon shekaru 40 na jamiyyar Kenya African National Union,Gwamnatin ta Mwai Kibaki za kuma ta farfado da tattalin arzikin kasar daya tabarbare a tsawon wannan lokaci,tare da tabbatar da cewa komai na fannin rayuwar bil adama a kasar na gudana yadda ya kamata.

To amma kuma,kash sai gashi tunanin masu ilimin kasar da kuma sauran alumma na wannan kasa ta Kenya na neman zama mafarki,sakamakon shekaru daya da gwamnatin ta Mwai Kibaki tayi ba tare da cimma wani abin azo a gani ba,dangane da kyautatawa alummar kasar tare da cika wasu alkawarurruka da jamiyyar tasa ta NARC ta dauka a lokacin gudanar da kamfe na neman shugabancin kasar.

Da farko dai a ganin masu nazarin abin da kaje yazo a kasar ta Kenya,gwamnatin Mwai Kibaki ta gudanar da bikin cikarta shekara guda a gadon mulki ne ta hanyar rushe jamiyyar NARC,wacce a karkashinta ne ya samu cimma gaci a zaben shugaban kasar daya gabata,koda yake a dalilin da Kibaki ya bayar na rushe jamiyyar shine sakamakon rikice rikice dake faruwa a tsakanin kungiyoyin da suka taru sukayi gamayyar hada wannan jamiyya ta NARC,wanda hakan yasa ta kaima cimma gaci.

Babban dai alkawarin da wannann jamiyya ta NARC ta daukarwa jama,ar kasar ta Kenya lokacin gudanar da kamfe na shugabancin kasar,shine na tabbatar da kafuwar sabon kundin tsarin mulkin kasa a acikin kwanaki dari da hawanta gadon mulki,na biyun sa kuma shine bayar da ilimin firamare kyauta,na uku kuma samar da aikin yi ga alummar kasa a kalla guda dari biyar,gami da kawo karshen cin hanci da kuma rashawa a fadin kasar baki daya.

To,amma kuma a hannu daya a cewar wani maikaci na kasar ta Kenya mai suna,Kitheka Mombo, daga cikin wadan nan alkawarurruka na sama babu daya da wannan gwamnati ta kibaki tayi kokarin cikawa in banda bayar da ilimin firamare kyauta,wanda shima a cewar sa yake fuskantar wasu matsaloli nan da can.

A cewar rahotanni da suka iso mana kuwa,rikice rikice a tsakanin kananan jamiyyun da suka hadu suka tayar da jamiyyar ta NARC ya samo asali ne sakamakon irin tafiyar hawainiyar da gwamnatin ta Kibaki keyi dangane da aiwatar da alkawarurrukan data dauka a lokacin gudanar da kamfe lokacin zaben shugaban kasar,wanda hakan ya haifar wa kungiyoyin gudanar da tarurruka na tattauna hanyoyin yiwuwar kirkiro ofishin firaminista.

Jamiyyar dake kann gaba wajen ganin hakan ya tabbata itace ta LDP,wacce itace kusan babba a cikin hadin gambizar yarjejeniyar da aka kulla,a tsakanin jamiyyun don tayar da jamiyyar da zata kalubalanci jamiyyar adawa ta ZANU a lokacin gudanar da zaben shugabancin kasar. A dai farko farkon watan disanma na shekara ta 2003 ne Mwai Kibaki ya bayar da sanarwar,cewa a watan yuni na shekara ta 2004,za,a tabbatar da kafuwar kundin tsarin mulkin kasar,to amma wannan kalami na Kibaki bai samu karbuwa ba a gun da dama daga cikin mutanen kasar ta Kenya,musanmamma bisa la,akari da abubuwan da suka faru a baya. A wata sabuwa kuma,a cewar wani malamin jami,a na kasar mai suna,Mwiti Nyanga cewa yayi,saurin yin fushi shike kawo dana sani,kibaki nada lokaci mai tsawo daya rage masa,wanda a lokacin zai iya gudanar da wadan nan abubuwa da ake zargin sa da kin cikasu,domin kuwa a cewar malamin koda birnin Rom na italiya ba,a gina shi rana daya ba,a don haka idan akabi kibaki a hankali za,a samu cimma nasarar abin da ake nema.

 • Kwanan wata 31.12.2003
 • Mawallafi Ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvmp
 • Kwanan wata 31.12.2003
 • Mawallafi Ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvmp