Siyasa a Faransa ta dauki sabon salo | Labarai | DW | 02.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siyasa a Faransa ta dauki sabon salo

Shugaban Faransa ya kauce daga neman wa'adi na biyu na mulki sakamakon rashin farin jini da matsaloli da suka dabaibaye gwamnatinsa.

Shugaba Francois Hollande na kasar Faransa ya bayyana cewa ba zai sake neman shugabancin kasar a zaben shekara mai zuwa na 2017 ba. Shugaban ya fadi haka ne lokacin da yake jawabi kai tsaye daga fadar shugaban kasa ta Elysée. Dan shekaru 62 a duniya da ya are kan karagar mulki karkashin jam'iyyar gurguzu ya ce da muguwar rawa gwamma kin tashi. Hollande ya zama shugaban Faransa na farko cikin rabin karni da ya yi wa'adi daya kacal, ba tare da sake neman wa'adin mulki ba.

Yanzu akwai yuwuwar Firaminista Manuel Valls na kasar ta Faransa ya kasance dan takara a jam'iyya mai mulki, sai dai sakamkon rarrabuwar kai a cikin jam'iyyar zai yi wuya ya kai zagaye na biyu a zaben shugaban kasa mai zuwa.