Siyasa a Afirka: 'Yan adawa na har abada?
Ba fusakun shugabannin da suka dade suna mulki a nahiyar Afirka ne kawai ake gani ba, su ma kansu 'yan adawar basu sauya ba. Sune dai wadanda suka dade suna fafutukar kawo sauyi a irin wadannan kasashe.
Zimbabwe: Morgan Tsvangirai da Mugabe
Tsohon mai hakar ma'adinan ya kasance dan adawa na din-din-din ga shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe da ya dade a gadon mulki. Ya kafa jam'iyyar adawa ta "Movement for Democratic Change" an sha kamashi da cin zarafinsa. An ma taba barazanar wurgo shi daga kan hawa na 10 na bene ta taga. Bayan zaben 2008 mai cike da rudani, Tsvangirai ya sa hannnu a kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka da Mugabe.
Masu yakin sunkuru a Mozambik
Ya na daya daga cikin wadanda suka dade suna adawa a Afirka: Afonso Dhlakama ya fara jagorancin mayakan sunkuru na kungiyar RENAMO a shekara ta 1979 yayin yakin basasa a Mozambik. Daga bisanin kungiyar RENAMO ta koma jam'iyyar siyasa. Har yanzu Dhlakama na nan a kan bakansa, ya ce a shirye yake ya sake daukar makami. Ya dai tsaya takarar shugabancin kasar sau biyar ba tare da samun nasara ba.
Tsohon minista a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango ya zama dan adawa
Etienne Tshisekedi ya zama ministan shari'a tun kafin ya kammala karatu a jami'a. Daga baya ya zama dan kwango na farko da ya sami digiri a fannin shari'a. Ya yi aiki karkashin shugaba Mobutu Sese Sekou amma daga baya ya zama mai adawa da gwamnati an kuma sha kama shi. Ya zama jagoran adawa tun shekara ta 2001. A shekara ta 2011 ya sha kaye lokacin da ya tsaya takara da shugaba Joseph Kabila.
Kenya: Siyasa a matsayin gado
Raila Odinga dan tsohon mataimakin shugaban kasar Kenya na farko, ya sha alwashi kana yana da fatan zama shugaban kasa. Tare da babansa da dan uwansa, ya kasance dan majalisa. Sai dai bai taba yin biyayya ga jam'iya ba, sau hudu yana sauya sheka. Bayan ya sha kaye a zaben 2013, ya je kotu domin kalubalantar sakamakon zaben, sai dai bai yi nasara ba.
Babban makiyi ga mahukuntan Yuganda
Kizza Besigye ya kasance na hannun dama kuma mafi kusanci ga shugaban Yuganda Yoweri Museveni kana likitansa. A yanzu ya kasance babban makiyi ga mahukuntan kasar tun bayan da ya ayyana bukatarsa ta zama shugaban kasa. An sha zarginsa da laifuka da dama, an kama shi tare da nada masa duka. An tuhume shi da cin amanar kasa tare da shirya zanga-zangar adawa da tazarcen Museveni a shekara ta 2016.
'Yan adawar da suka fi yin fice a Chadi
Saleh Kebzabo daga hagu da Ngarlejy Yorongar na wakiltar jam'iyyun siyasa, sun dade suna adawa tare domin kawo sauyi a kasar. Sai dai hadin kansu ya wargaje gabanin zaben da aka gudanar a bana, bayan da suka gaza amincewa kan yadda za su taimaki juna a zaben. An sake zabar Shugaba Idriss Deby da ya kwashe shekaru 26 a kan karagar mulki a matsayin shugaban kasa a karo na biyar.
Shugaban kasar da ya ayyana kansa a Togo
Jean-Pierre Fabre ya kasance dan adawa a kasar Togo. Shi ne shugaban jam'iyyar "National Alliance for Change", ya kuma tsaya takarar shugaban kasa sau biyu. Bayan da ya sha kaye a shekara ta 2015, ya fusata inda ya yi watsi da sakamakon zaben inda ya ce an tafka magudi. Ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar da aka zaba, sai dai bai samu nasara ba.
Nasara a karo na uku ga Akufo-Addo na Ghana?
Mahaifin Nana Akufo-Addo ya yi shugabancin kasar Ghana a shekarun 1970, sai dai har yanzu bai hakura ba. Mutane da dama a Ghana na jin takaicin yadda ya ke neman shugabanci ido a rufe. Ba za su iya yin mu'amala da mtumin da ya kasance babba ba. Ya na son sake tsayawa takara a karo na uku a watan Nuwamba. Zai iya zama yunkurinsa na karshe kasancewar kan 'yan jam'iyyarsa ba hade yake ba.