1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: 'Yan tawaye za su je taron Geneva

Ahmed SalisuJanuary 30, 2016

Kungiyar 'yan tawayen Siriya ta ce wakilanta sun kama hanya zuwa birnin Geneva domin yin nazari kan ko za su shiga taron da ake kan rikicin Siriya.

https://p.dw.com/p/1HmF5
Genf Friedensverhandlungen zu Krieg in Syrien
Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Tawagar dai ta kunshi mutane 17 kuma mai magana da yawun gamayyar 'yan tawayen ya ce za su fara sanya idanu don ganin kamun ludayin gwamnatin Bashar Assad dangane da dakatar da afakawa yankunan da 'yan adawa ke da karfi.

Wannan sanarwar da kungiyar ta fidda ta kawo karshen halin rashin tabbas din da ake ciki na yiwuwar halarta taron ko akasin haka wanda ke gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Kasashen duniya dai sun nuna jin dadinsu dangane da hakan, inda suka bukaci da a hau kan teburin sulhu da nufin samun mafita a siyasance da za taimaka wajen kawo karshen rikicin Siriya.