Siriya ta yi gargaɗi mambobin kwamitin sulhu da su guji tsoma baki a hulɗoɗi tsakaninta da Lebanon. | Labarai | DW | 10.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya ta yi gargaɗi mambobin kwamitin sulhu da su guji tsoma baki a hulɗoɗi tsakaninta da Lebanon.

Muƙaddashin ministan harkokin wajen Siriya, Fayssal Mekdad, ya gargaɗi mambobin kwamitin sulhu na Majjalisar Ɗinkin Duniya, musamman ma Amirka, da su guji tsoma mata baki a hulɗoɗinta da ƙasar Lebanon. Ministan ya yi wannan kiran ne, a wata fira da ya yi da amneman labarai, a daidai lokacin da kwamitin sulhun ke shirin zartad da wani ƙuduri, wanda zai bukaci Siriyan da ta ƙulla hulɗar diplomasiyya da Lebanon, sa’annan kuma ta zayyana iyakarta da ƙasar mai makwabtaka da ita, don cika ƙa’idojin wani ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniyar ta amince da shi a cikin watan Satumban shhekara ta 2004. Ƙuduri mai lamba 1559, ya yi kira ne ga duk dakarun ƙetare da su fice daga ƙasar ta Lebanon, da kuma kwance wa ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ɗamara, don bai wa gwamnatin Lebanon ɗin damar yaɗa angizonta a duk faɗin ƙasar.