Siriya ta ƙaryata wasu rahotannin da ke nuna cewa ta amince da girke dakarun ƙungiyar EU a kann iyakarta da Lebanon. | Labarai | DW | 10.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya ta ƙaryata wasu rahotannin da ke nuna cewa ta amince da girke dakarun ƙungiyar EU a kann iyakarta da Lebanon.

Siriya ta ƙaryata wasu rahotannin da ke bayyana cewa, ta cim ma yarjejeniya da ƙasashen ƙungiyar Haɗin Kan Turai don su girke dakarunsu a kann iyakarta da Lebanon. Da can dai Firamiyan Italiya Romano Prodi, ya bayyana cewa shugaba Bashar al-Assad na Siriyan ya amince da girke jami’an sa ido a kan iyakar ƙasarsa da Lebanon don aiwatad da takunkumin makamai da aka sanya wa ƙungiyar Hizbullahi. A ran juma’ar da ta wuce ne kuma, babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ya ce shugaban Siriyan ya yi masa waya, inda ya tabbatar masa da cewa, zai taimaka wajen sa ido a yankunan iyakar.