1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Kwashe 'yan tawaye daga Aleppo

Salissou Boukari
December 15, 2016

Gwamnatin Siriya ta soma fitar da mutanen da ke makale a yankin da ya rage a hannun 'yan tawaye na gabashin Aleppo bayan cimma wata yarjejeniya tsakanin bangarorin da ke da hannu cikin lamarin.

https://p.dw.com/p/2UJrZ
Syrien Krieg - Evakuierungen in Aleppo
Hoto: Reuters/A. Ismail

Shaidun gani da ido sun ce an ga fararan motocin daukan marasa lafiya, da kuma motocin bas-bas masu launin tsanwa da tsakiyar ranar Alhamis na ta shiga yankunan da 'yan tawaye suke domin fitar da su, musamman ma wadanda suka samu raunuka da iyalansu. Tuni dai kungiyar agaji ta Red Cross da ke kasar ta Siriya ta tabbatar da hakan, inda ta ce tuni mutane suna ta shiga cikin motocin, kuma motocin za su yi ta zuwa da zowa.

A cewar gidan telebijin din kasar ta Siriya, wannan aiki ya shafi akalla 'yan tawaye 4000 da iyallansu. Tun dai a shekara ta 2012 ne 'yan tawayen na Siriya suka kwace birnin na Aleppo da ke a matsayin birni na biyu mafi girma a kasar, kuma kwace shi a halin yanzu ba karamin koma baya ne ga 'yan tawayen ba.