1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Sanyin hunturu na kashe 'yan gudun hijira

Mahmud Yaya Azare
January 26, 2018

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna takaici kan mace-macen da ake samu a sansanonin da aka tsugunar da daruruwan 'yan gudun hijirar Siriya a kasashen da ke makwabtaka da ita.

https://p.dw.com/p/2rVTE
Libanon Schneefall syrische Flüchtlinge
Daruruwan 'yan gudun hijra Siriya ke zaune a wannan sansaniHoto: Reuters

Guguwa daga teku ce ke bugawa a sansanin 'yan gudun hijirar Beka da ke kan iyakar Siriya da Labanan, sansanin da dusar kankara ta yi kusan binne shi. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta ce guguwar da aka yi wa lakabi da Ziynah ta halaka kimanin mutane 30 tun farkon soma sanyin hunturun wanda galibinsu kananan yara ne da kuma tsofaffi.

Baya ga haka dusar kankara da ruwan sama da ake ta yi a yankin a 'yan kwanakin nan, ya sa cabi ya cika ko ina a matsugunan jama'ar da yaki ya tilastawa tserewa daga gidajensu. 'Yan gudun hijira sun bayyana halin kunci da suka sami kansu ciki na rashin samun abinci mai gina jiki baya ga jikewarwuraren kwanciyarsu a sanadiyar ruwan, ga kuma tsananin sanyi.

Libanon Schneefall syrische Flüchtlinge
Dusar kankara a sansanin 'yan gudun hijraHoto: Reuters

Dr Ali Haraki, likita ne na hukumar kai agajin gaggawa, ya ce haduwar sanyi da rashin samun abinci mai kyau, ka iya mai da karamin ciwo ya zama annoba.

"Rashin samun abinci mai gina jiki, idan ya hadu da sanyi  da kuma zubar kankara zai iya karya garkuwar jikin yara da tsofaffi, yadda cutattuka za su iya bazuwa ba kakkautawa. Ya zama wajibi a kawo daukin gaggawa don yanzu haka cututtukan tari da matsalolin numfashi da Asma suna ta bayyana, yara da dama na fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin na'urar shakar numfashi”

Syrien Flüchtlinge in Libanon
Wani bangaren na sansanin Hoto: Reuters

A daya bangaren kuwa wani jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira a Turkiya, Sander Van Niekerk, ya ce farmakin da Turkiyya ta fara kai wa yankin Afrin na Kurdawa a Siriya, ya tilasta wa 'yan gudun hijira kimanin dubu 50 da ke kokarin tsira da rayukansu neman mafaka a dajin Allah, yunwa da sanyin huturun na neman halaka su.