Christian Kwessi na son ganin ya saukaka al'amura ga mutanen da ke larurar makanta a birnin Doula da ke jamhuriyar Kamaru. Dabarun da yake amfani da su wajen yin haka shi ne ta hanyar fadarkar da hukumomi da wasu fina-finai da ya shairya wa makafi da masu gani ko da dai ya fuskanci kalubale da dama.