Singapore ta rataye wani Australiya a kan laifin sumogar miyagun kwayoyi | Labarai | DW | 02.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Singapore ta rataye wani Australiya a kan laifin sumogar miyagun kwayoyi

Kasar Singapore ta zartas da hukuncin kisa a kan wani dan kasar Australiya a kan laifin sumogar gram 400 na miyagun kwayoyin heroin, duk da rokon da gwamnatin Australiya ta yi na a yi masa afuwa. An rataye mutumin mai suna Nguyen Toung Van dan shekaru 25 a duniya a gidan kurkukun birnin Changi. FM Australiya John Howard ya ce rataye mutumin zai shafi dangantaka tsakanin kasar sa da Singapore. Babban lauyan gwamnatin Australiya Philip Ruddock ya bayyana aiwatar da hukuncin kisan da cewa wani hali ne na dabbanci. A ziyarar da ya kai birnin Berlin a jiya alhamis an jiyo FM Singapore Lee Hsien Loong na cewa ko kadan ba za´a yiwa Nguyen Van wani sassauci ba. A cikin shekara ta 2002 aka kame Nguyen Van wanda dan asalin Vietnam ne a filin jirgin saman Singapur dauke da miyagun kwayoyin na heroin.