1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sin zata sanar da samfurin sinadrin cutar murar tsuntsaye

December 2, 2006
https://p.dw.com/p/BuZQ

Kasar sin tayiwa sabuwar shugabar hukumar kula da lafiya ta mdd cewa,zata gaggauta raba sanfurin sinadrin murar tsuntsaye ,sakamakon zargin da akewa kasar da kawo koma baya,a kokarin gano tare da shawo kann annobar cutar.Kwararriya ta fannin cutar murar tsuntsaye ta kasar Sin,Margaret Chan,wadda aka zaba a watan nuwamba,a matsayin jagorar WHO,a kwannan ta kammala rangadin aiki na kwanaki 4 a kasar,inda ta gana da shugaba Hu jintao,da premier Wen Jiabao,da ministan lafiya Gao Qiang.Margret Chan tace,sakamakon ganawarta da shugabannin uku na nuni dacewa,sun fahinci bukatar gaggauta sanar da wannan sanfurin kwayoyin Cuta.Ta kara dacewa kasar Sin ta kashe kudade masu yawa wajen inganta ,bincikenta kann cututtuka da ake iya yadawa.A watan daya gabata nedai kasar Sin tayi alkawarin sanarwa wa duniya samfurin sinadran murar tsuntsaye,akokarin da ake na shawo kann annobar yaduwarta.