Sin da ƙasashen Afirka sun kammala taron ƙolinsu a birnin Beijin. | Labarai | DW | 05.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sin da ƙasashen Afirka sun kammala taron ƙolinsu a birnin Beijin.

Sin da ƙasashen Afirka sun kammala taron ƙolinsu a birnin Beijin. Rahotanni dai sun ce taron, shi ne mafi girma tsakanin ɓangarorin biyu da aka taɓa yi, tun juyin juya halin ’yan kwaminis na Sin a cikin shekarar 1949. An kuma sanya hannu kan wata gagarumar yarjejeniyar cinikayya ta dola biliyan ɗaya da ɗigo 9, tsakanin kamfanoni 12 na Sin ɗin da ƙasashen nahiyar Afirka. Shugaba Hu Jintao na Sin ɗin kuma, ya ɗau alkawarin bai wa ƙasashen nahiyar Afirkan rancen kuɗaɗe na kimanin dola biliyan 5, sa’annan kuma da riɓanya taimakon da take bai wa ƙasashen Afirkan sau biyu, kafin yanzu zuwa shekara ta 2009.

Ita dai Sin tana bukatan albarkatun ƙasa ne daga nahiyar ta Afirka, kamarsu man fetur da hayaƙin gas da ma’adinai, don bunƙasa tattalin arzikinta.