1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sin da ƙasashen Afirka sun sanya hannu kann wata gagarumar yarjejeniyar cinikayya.

November 5, 2006
https://p.dw.com/p/BudR

Sin da ƙasashen Afirka sun sanya hannu kan wata gagarumar yarjejeniyar cinikayya ta dola biliyan ɗaya da ɗigo 9, a ranar ƙarshe ta taron ƙolin shugabannin ƙasashen ɓangarorin biyu da ake gudanarwa a birnin Beijing. Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya yi marhabin da sanarwar da Sin ɗin ta bayar, ta cewa za ta riɓanya taimakon da take bai wa ƙasashern Afirkan sau biyu, kafin yannzu zuwa shekara ta 2009.

Wani babban jami’in Majalisar ya ce yayin da ƙasashen Afirkan ke nuna ƙwazo wajen warware matsalolin da suke huskanta, za su kuma iya yin kwaikwayo da Sin wajen bunƙasar tattalin arzikinsu da kuma yaƙan talauci.