Shugabar manufofin ƙetare ta EU zata kai ziyarar gani da Ido zuwa Gaza | Siyasa | DW | 07.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugabar manufofin ƙetare ta EU zata kai ziyarar gani da Ido zuwa Gaza

EU na buƙatar farfaɗo da tattaunawar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

default

Catherine Ashton Shugabar lura da manufofin ƙetare ta ƙungiyar tarayyar Turai.

Yan watanni bayan da aka naɗata a matsayin shugabar kula da manufofin ketare na ƙungiyar tarayyar Turai, Catherine Ashton ta sanar da cewa tana tattaunawa da hukumomin Israila game da ziyarar da zata kai zuwa Gaza a rangadin da zata yi zuwa yankin Gabas Ta Tsakiya a cikin wannan watan.

Ziyarar dai na da nufin farfaɗo da shawarwarin zaman lafiya tsakanin Israila da Falasɗinawa. Ƙungiyar tarayyar turan na fatan shiga kaín da naín wajen cimma sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu.

Shugabar lura da manufofin ƙetare ta ƙungiyar tarayyar turan Catherine Ashton tace tana fatan kai ziyara yankin zirin Gaza a tsakiyar wannan watan na Maris "Ina so in kai ziyara Gaza domin na ganewa idanuna abin da ya faru da dumbin kuɗaɗen gudunmawa da muka bayar. Ina kuma buƙatar tattaunawa da jamaár gari game da tasirin tallafin da muke basu. Wannan yana da matuƙar muhimmanci a garemu".

Waffenruhe in Gaza Familien am Strand

Rayuwar Falasɗinawa a Gaza.

Ita dai ƙungiyar tarayyar turai tana daga cikin rukunan nan huɗu na Quartet waɗanda ke shiga tsakani domin wanzar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya. Rukunin na Quartet ya ƙunshi ita kanta ƙungiyar ta EU da Amirka da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Rasha.  

A kan haka ne Ministan harkokin wajen Jamus Guido Wester Welle yayi tsokaci yana mai cewa " Muna buƙatar gabatar da kanmu a matsayin tarayyar turai da kuma ƙarfafa ƙudirinmu na wanzar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya. A saboda haka muna kira ga dukkan ɓangarorin biyu su jingine banbance banbancen dake tsakaninsu yadda zaá sami tattaunawa mai maána".

Ƙungiyar ta tarayyar turai dai ta buƙaci hanzarta kafa ƙasar Falasɗinawa. Sai dai kuma halin da ake ciki a Gaza inda yan gwagwarmayar Hamas ke riƙe da ragamar shugabanci, waɗanda kuma suka yi watsi da tattaunawa da Israila na haifar da damuwa. A bara ne dai aka dakatar da tattaunawar zaman lafiyar ta gabas ta tsakiya sakamakon ɓarin wutar da Israila ta yi a Gaza a yaƙin da sojojinta suka gwabza da mayaƙan Hamas. Ministan harkokin wajen Sweden Carl Bildt ya baiyana halin killacewar da aka yiwa yankin zirin Gaza da cewa ba mai karɓuwa bane. Shima Ministan harkokin wajen Luxemburg Jean Asselborn ya yi kira ga Israila ta dakatar da cigaba da faɗaɗa matsugunai da take yi a yankunan da ta mamaye. " Wannan a ganina wata manuniyace ga Israila cewa gamaiyar ƙasa da ƙasa na buƙatar ganin wani tartibi a ƙasa yadda zaá cimma masalahar kafa ƙasashe biyu da zasu zauna daura da juna cikin girma da arziki.

Mawallafa: Bernd Riegert/Abdullahi Tanko Bala Edita Yahouza Sadissou Madobi