Shugabar Jamus ta jaddada matakan yaki da taaddanci | Labarai | DW | 02.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabar Jamus ta jaddada matakan yaki da taaddanci

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace ba zaa kawar da yuwuwar cigaba da amfani da karfin soji wajen yaki da taaddanci ba.

A lokacinda take jawabi a wata liyafa da aka shiryawa jamian diplomasiyya a birnin Berlin shugabar tace yaki da taddanci abune dake bukatar amfani da siyasa da tattalin arziki idan abu kuma yaci tura sai ayi amfani da matakan soji amma tace amfani da matakan sojin wajibi ne ya kasance karkashin ikon majalisar dinkin duniya.