1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabar gwamnatin Jamus za ta fara ziyara a Afirka

October 6, 2016

A lokacin ziyarar shugabar gwamnatin za ta gana da shugabanni na kungiyoyin fafutika da masu tallafa wa 'yan gudun hijira .

https://p.dw.com/p/2QxUL
Bundestag Kongo Einsatz für die Bundeswehr Angela Merkel
Hoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta kai ziyara kasashen Mali da Nijar da Habasha dan tattaunawa da shugabanni da kasashensu ke zama hanyoyi da bakin haure ke bi a kokari na danganawa da kasashen Turai. Wata majiyar gwamnati ta bayyana haka ga kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA a birnin Berlin fadar gwamnatin ta Jamus a ranar Alhamis din nan.

A ranar Lahadi ne dai Shugabar gwamnatin Merkel za ta fara wannan ziyara ta kwanaki uku inda a lokacinta za ta halarci bikin bude ginin Kungiyar Tarayyar Afirka da Jamus ta dauki nauyin ginawa a birnin Addis Abeba babban birnin kasar Habasha, za kuma ta gana da sojojin Jamus a Mali da Nijar wadanda ke zama wani bangare na dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali. Har ila yau a wannan ziyara shugabar gwamnatin za ta gana da shugabanni na kungiyoyin fafutika da masu tallafa wa 'yan gudun hijira .

A shekarar 2015 dai Jamus ta karbi bakuncin 'yan gudun hijira sama da dubu dari takwas mafi yawa daga Siriya da Afghanistan da  wadanda ke gujewa talauci musamman daga kasashen Arewacin Afirka.