Shugabar Brazil na ci gaba da nuna turjiya | Labarai | DW | 19.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabar Brazil na ci gaba da nuna turjiya

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta sha alwashin yaki da duk wani yunkuri daga 'yan majalisar dokokin da majalisar dattawa na tsigeta daga mukaminta.

Shugabar wacce ake zargi ta da badakalar harkokin kudaden kasar, ta kuma ce za ta yi duk abin da ya wajaba wajen ganin kujerar ba ta sullube mata ba.

Kazalika Thomas Truman wanda ya taba yin aiki da Shugaba Dilma Rousseff a matsayin mai magana da yawu ta ya bayyana cewar za ta tsallake tarkon tsingewar.

"Ina ganin Shugabar kasar sai inda karfin ta ya kare. Dilma Rousseff ta tsallake wasu mawuyatan yanayi a rayuwarta, da suka hada da lokutan da ake mata zanga- zanga a shekara ta 2013 da kuma lokutan zabe."