Shugabannin tarayyar Turai sun kuduri aniyar samar da masalaha tsakaninsu | Labarai | DW | 28.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin tarayyar Turai sun kuduri aniyar samar da masalaha tsakaninsu

Duk da bambamce-bambamce game da manufofin tattalin arziki da na zamantakewa shugabannin kasasken KTT sun kuduri aniyar cimma wata madafa a takaddamar da suke yi akan kasafin kudin kungiyar a wannan shekara. Shugaban gwamnatin Jamus mai barin gado Gerhard Schröder ya ce yanzu sun kusa cimma wata yarjejeniya bisa manufa bayan shawarwarin da shugabannin kungiyar suka yi a birnin London game da aiwatar da canje canje da suka dace da gasar cinikaiya na kasa da kasa. A lokaci daya Schröder ya ce sabuwar gwamnatin Jamus ba zata iya daukar alkawarin ba da karin gudummawar kudi ba. Da farko dai hukumar kungiyar EU ta ba da shawarar zuba kudi Euro miliyan 500 a duk shekara cikin wani asusu, don tinkarar duk wani kalubale da za´a fuskanta sakamakon canje-canjen da ake aiwatarwa.