Shugabannin SADC sun kaddamar da sabuwar rundunar wanzar da zaman lafiya | Labarai | DW | 17.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin SADC sun kaddamar da sabuwar rundunar wanzar da zaman lafiya

Shugabannin kasashen kudancin Afrika sun kaddamar da wata rundunar wanzar da zaman lafiya ta musamman wadda zata rika aiyukan wanzar da zaman lafiya da kwance damara a yankunan da aka kawo karshen rikici nahiyar.Shugaban kasar Zambia Levy Mwanawasa ya kaddamar da rundunar wajen taron kungiyar raya kasashen kudancin Afrika a birnin Lusaka.

Kaddamar da rundunar yana bangare ne na kokarin samarda rundunar yan kwana kwana na Afrika a 2010 karkashin MDD da AU da kuma SADC.