1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin nahiyar Afrika a Amurka

September 23, 2004

Ana cigaba da tattaunawa da shugabannin nahiyar Afrika a New york can Kasar Amurka .

https://p.dw.com/p/BvgE
Hoto: James Marshall

Shugabannin dai sun karrama wannan shugaban ne a birnin new york can Kasar Amurka a cigaba da taron mashawartar majalisar dinkin Duniya da ake gudanarwa a yanzu haka a kasar ..Bugu da kari dai shugabannin sun nuna kaico na yarda ake cigaba da fuskantar matsalar tashe tashen hankula a nahiyar baki daya kama daga lardin darfur a can Kasar Sudan da kuma sauran sassan nahiya baya ga matsalar cutar kanjamau ko ceda da take neman samun gindin zama a yankin na Afrika ..Shugabanin nahiyar dai sun dagawa shugaba Wade tuta bisa rawar daya taka na kawo karshen cin zarafin bakaken fatun lardin na darfur a kasar sudan a yayin da yan kungiyar janjawed na kasar ke lugudan wuta ga bakaken fatu a lardin na darfur batare kuwa da kakkautawa ba .an dai kwashe sama da watanni 19 ana fafaTAWA A TSAKANIN BBANGARORIN BIYU wanda yayi sanadiyar mutuwar a kalla mutane sama da dubu 50 a yayin da daruruwa sukai kaura zuwa wasu yankunan cikin kasar da kuma wajenta ..A jawabinsa na karbar wannan lambar yabo shugaba Wade na Senagal ya bukaci karin waadi ga kungiyar taraiyar Afrika domin samun damar kwance damarar yaki ga yayan kungiyar ta janjawed domin samun kwanciyar hankali a kasar ta sudan ..Yace zaa cigaba da tuntubar juna har sai hakan ya cimma ruwa gta fannin tattaunawa inda kuwa hakan ta faskara to babu shakka zaa yi anfamni da dakarun kasashen Nahiyar domin cimma manufar da aka sanya a gaba a kann batun na Darfur ..Tuni dai kwamitin tsaro na Mdd ya bukaci kungiyar taraiyar afrika data kasra kaimi na kawo karshen wannan tataburza a tsakanin yabn tawayen na darfur da kuma bakaken fatu daa halin yanzu ke cikin halin ni kyasu ..Tun ba yau ba dai ake zargin gwamnatin kasar ta sudan da marawa kungiyar yan tawayen baya wanda kuma a hannu guda ta musanta hakan ..A yanzu haka dai kungiyar ta aU a takaice nada a kalla dakarun soji 80 wadanda ke sanya ido domin sanin yarda halin lardin ke ciki baya ga dakarun kwantar da tarzoma sama da dari ukku daga kasashen na Afrika a kasar ta sudan ..Daya daga cikin manyan jamian gwambnati a nahiyar ta Afrika wanda baiso a bayyana sunan saba yace ana bukatar goyan baya daga MDd da kuma kasashen yamma musamman ta fannin ababan hawa da kudade domin kara aikewa da dakaru zuwa ga lardin na darfur .A wani taro da yayan kwamitin tsaro na mdd suka gudanar a ranar asabar data gabata sun tabbatar da sake wani zama na musamman a nan gaba domin kakabawa kasar ta sudan takunkumin sayar da man fetur a kasashen ketare matukar batun darfur bai cimma matsaya daya ba .WAta majiya dai na cewa tattaunawar data wanzu a tsakanin kasashen Afrika a wannan mashawarta sunfi mayar da hankali ne kacokam kann batun yaki da cutar kanjamau ko ceda baya ga fatara da yunwa dake cigaba da kassara nahiyar baki daya