Shugabannin kasashen Duniya sun yi kira ga samad da kwanciyar hankali bayan hare-haren da aka kai a kan ofisoshin jakadancin Denmark a wasu kasashen musulmi. | Labarai | DW | 06.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin kasashen Duniya sun yi kira ga samad da kwanciyar hankali bayan hare-haren da aka kai a kan ofisoshin jakadancin Denmark a wasu kasashen musulmi.

Game da zanga-zangar nuna adawa ga batancin da aka yi wa annabi Muhammmadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, inda al’amura suka tabarbare a kasashen Lebanon da Siriya a karshen mako, har aka cinna wa ofisohin jakadncin kasar Denmark a manyan biranen Damascus da Beirut wuta, shugabannin kasashen duniya sun yi kira ga samad da kwanciyar hankali, don shawo kan wannan rikicin.

Da farko dai, babban sakataren Majalisar dinkin Duniya Kofi Annan ya bayyana damuwarsa ga yadda al’amura ke ta kara tabarbarewa. Ya kuma yi kira ga masu zanga-zangar da su yi taka -tsantsan wajen bayyana bacin ransu, ba tare da ta da tarzoma ba. Amma kasar Iran, wadda ta ce tana nazarin yadda za ta tafiyad da harkokin cinikayyarta da kasashen da aka buga hotunan batancin a cikinsu, ta lashi takobin mai da martani ga duk masu bin wani sabon salo na nuna kyama ga addinin islama.

Ministan harkokin wajen Faransa, Phillipe Douste-Blazy, shi ma ya yi kira ga kasashen Larabawa da su nuna sassauci ga abin da ke wakana a halin yanzu.

A cikin wata makala ta hadin gwiwa da suka buga a jaridar nan ta International Herald Tribune, Firamiyoyin kasar Turkiyya da na Spain, Tayyib Erdogan da Jose Luis Rodriguez Zapatero, sun bayyana cewa, buga hotunan zanen siffanta annabi Muhammadu, salal lahu alaihi wassalam, a cikin wasu jaridun kasashen Turai, wato wani abin matukar ta da hankali ne ga musulmi. Sabili da haka ne ya zama wajibi ga duk masu fada a ji duniya baki daya, da su yi duk iyakacin kokarinsu wajen ganin cewa, an warware wannan matsalar cikin ruwan sanyi, saboda idan aka kyale al’amura suka tabarbare, a karshe duk kowa ma asara zai yi.

Duk da zanga-zangar, da kuma kokarin da ake yi na shawo kan wannan rikicin dai, kasar Ukraine, ita ma ta shiga sahun kasashen da ke ci gaba da buga hotunan zanen batancin. Rahotanni sun ce an buga hotuna a cikin wasu jaridun kasar na yau. Ban da dai Ukraine din, kasashen da jaridunsu suka buga hotunan sun hada ne da Bulgeriya, da Faransa, da Jamus, da Italiya, da Sppain, da Switzerland, da Hungary, da New Zealand, da Austreliya da Poland da kuma Amirka.