Shugabannin Israila sun bada umurnin sake kutsawa Gaza | Labarai | DW | 11.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin Israila sun bada umurnin sake kutsawa Gaza

Jamian tsaro a kasar Israila sun bada sanarwar cewa,mahukuntan kasar sun bada umurnin sake kutsawa cikin zirin Gaza,yayinda firaministan Israila da shugaban Palasdinawa sunki sassautowa daga matsayi da suka dauka akan wannan rikici na kwanaki 13 biyo bayan garkuwa da akayi da sojan Israila.

Firaministan Israila Ehud Olmert da ministan tsaro Amir Peretz sun bada umrni ga sojin Israilan da su sake kutsawa Gaza,inda zaa sake tura sojoji yankuan da tun farko basu shiga ba domin gano inda sojan yake boye.

Ya zuwa yanz dai sojojin na Israila sun shiga kudanci da arewacin Gaza hakazalika sun gabda shiga birnin Gaza.

A jiya litinin dai shugaban kungiyar Hamas Khaled Mashaal ya bukaci musayar fursunoni,amma Ehud Olmert yace yin hakan wani babban kuskure ne.

Palasdinawa 58 suka rasa rayukansu cikin wannan rikici.