Shugabannin Falasɗinawa na ci gaba da shawarwarin kafa sabuwar gwamnati. | Labarai | DW | 13.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin Falasɗinawa na ci gaba da shawarwarin kafa sabuwar gwamnati.

Ƙungiyar Hamas, mai jan ragamar mulkin Hukumar Falasɗinawa a halin yanzu da jam’iyyar Fatah ta shugaban Falasɗinawan Mahmoud Abbas, na ci gaba da shawarwarinsu na kafa gwamnatin haɗin ƙan ƙasa. Tuni dai wani kamfanin dillancin labaran Faransa, Agence France Presse, ya ruwaito cewa ɓangarorin biyu sun yarje kan naɗa sabon Firamiya. Amma har ila yau Hukumomin Falasɗinawan ba su tabbatad da wannan rahoton ba. Ana dai sa ran cewa Ƙungiyoyin Hamas da na Fatah za su cim ma daidaito wajen kafa sabuwar gwamnatin haɗin kai, wadda Amirka da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai za su amince da ita, abin da kuma zai janyo kawo ƙarshen takunkumin da suka sanya wa hukumar Falasɗinawan. Tun cikin watan Janairun wannan shekarar ne dai, ƙasashen Yamma suka sanya wa Falasɗinawan takunkumi, bayan da Ƙungiyar Hamas ta lashe zaɓen da aka gudanar. Amirka da Ƙungiyar EU dai na bukatar duk wata gwamnatin Falasɗinun da za a kafa ne ta amince da Isra’ila, sa’annan kuma ta dakatad da duk wasu tashe-tashen hankulla.