Shugabannin EU zasu sanya hannu sabuwar yarjejeniyar ƙungiyar | Labarai | DW | 13.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin EU zasu sanya hannu sabuwar yarjejeniyar ƙungiyar

Shugabannin ƙungiyar tarayyar Turai sun fara hallara a Lisbon babban birnin kasar Portugal don sanya hannu kan yarjejeniyar yiwa ƙungiyar EU canje canje. Yarjejeniyar zata maye gurbin daftarin kundin tsarin mulkin kungiyar wanda kasashen Netherlands da Faransa suka yi watsi da shi a wata ƙuri´ar raba gardama da suka gudanar a shekara ta 2005. Ana fatan cewa wannan yarjejeniyar zata sabunta hukumomin kungiyar tare da bin karin manufofi na demokuraɗiyya. To sai dai ba zata fara aiki ba har sai dukkan ƙasashe 27 membobin ƙungiyar sun sanya mata hannu. Ana sa ran kammala shirin sanya mata hannu a farkon shekara ta 2009 gabanin sabbin zabukan ´yan majalisar dokokin kungiyar ta EU. A kuma halin da ake ciki SGJ Angela Merkel ta bayyana yarjejeniyar da cewa wani harsashe ne ga wata sabuwar ƙungiyar EU a cikin ƙarni na 21.