Shugabannin EU sun yi maraba da sakamakon taron ƙolinsu a Brussels | Labarai | DW | 23.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin EU sun yi maraba da sakamakon taron ƙolinsu a Brussels

Shugabannin kasashen KTT sun nuna gamsuwa game da sakamakon taron kolin da suka gudanar a birnin Brussels akan yarjejeniyar daftarin tsarin mulkin kungiyar. Shugaban Poland Lech Kaczynsky ya yaba da sakamakon cewa wata nasara ce. Ita kuwa SGJ kuma shugabar kungiyar EU a yanzu, Angela Merkel cewa ta yi sakamakon zai bawa kungiyar wani sabon fasali. Sabon shugaban Faransa Nikolas Sarkozy cewa yayi an kammala aikin cikin tsanaki ba tare da yin watsi da bukatun kowa ba. Shugaban hukumar kungiyar EU Jose Manuel Barroso ya bayyana taron da cewa babban ci-gaba ne ga shirin fadada kungiyar.

O-Ton Barroso:

“In da ba´a cimma wata yarjejeniya ba, da ba za´a iya ci-gaba da fadada kungiyar ba domin wasu kasashe zasu nuna adawa. Saboda haka cimma wannan yarjejeniya gagarumin ci-gaba ne ga kasashe musamman ma Kuratiya.”