Shugabannin EU sun yi maraba da sabon kasafin kudin kungiyar | Labarai | DW | 17.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin EU sun yi maraba da sabon kasafin kudin kungiyar

Shugabannin kasashen tarayyar Turai sun nuna gamsuwa game da yarjejeniya da aka cimma akan yadda za´a tafiyar da harkokin kudin kungiyar EU. Musamman sabbin kasashen kungiyar EU daga gabashin Turai sun yi maraba da sakamakon taron kolin da aka gudanar a birnin Brussels. FM Poland Kazimierz Marcin-Kiwic ya ce Faransa da Jamus sun nuna a fili cewa suna goyon bayan kasar sa. Su kuma Sweden da Faransa sun yaba da matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka wanda ya ba da damar cimma wannan yarjejeniya. Shi kuwa a nasa bangaren FM Tony Blair cewa yayi nazarin da za´a yi akan kasafin kudin a shekara ta 2008 da ta 2009 zai ba da damar sabunta tsarin tafiyar da harkokin kudin kungiyar da ya dace da sauyin zamani. SGJ Angela Merkel ta bayyana yarjejeniyar da cewa wata alama ce mai karfafa guiwa.