1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin EU sun cimma masalaha kan gyaran daftarin doka

October 29, 2010

Shugabannin EU sun amince da yin kwaryakwaryar gyara ga kundin tsarin mulkin kungiyar

https://p.dw.com/p/PrbO
Daftarin kundin tsarin mulkin kungiyar tarayyar turai

Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar turai sun amince da yin yar kwarya kwaryar gyara bisa shawarar da Jamus ta bayar game da yadda za'a kare kasashen kungiyar daga sake fadawa rikicin kudi irin wanda kasar Girka ta shiga a farkon wannan shekarar. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tabbatar da hakan yau a Brussels. Kasashe 27 mambobin kungiyar tarayyar turan EU na kokarin samar da ingantaccen tsari ne akan lokaci gabanin taron da za su gudanar a cikin watan Disamba. Sai dai shirin da Jamus da Faransa suka gabatar na dakatar da yancin kada kuri'a ga dukkan kasar da ta karya ka'idar gibin kasafin kudi ya fuskanci kakkausar daga sauran kasashen. Dukkan wata shawara da taron zai tsayar dai na nufin yin gyara ga daftarin kundin tsarin mulkin kungiyar. An dauki tsawon shekaru goma kafin a sami daukacin kasashen 27 na kungiyar ta EU su amince da kundin tsarin mulkin wanda ake yiwa lakabi da Yarjejeniyar Lisbon.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu