Shugabannin Afirka sun watsi da wani shirin ciniki da EU | Labarai | DW | 09.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin Afirka sun watsi da wani shirin ciniki da EU

Shugabannin ƙasashen nahiyar Turai da takwarorinsu na nahiyar Afirka na dab da sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar dangantaka tsakanin nahiyoyin biyu, don kawo ƙarshe taron kolinsu a birnin Lisbon na ƙasar Portugal. Yarjejeniyar dai zata tanadi ƙarfafa haɗin kai a fannonin kwararar baƙin haure, hulɗar kasuwanci, makamashi, sauyin yanayi da kuma raya ƙasashe. To sai dai shugabannin ƙasashen Afirka da dama sun yi watsi da wani sabon shirin hulɗar cinikaiya wanda kungiyar tarayyar Turai ke bukata. Hakan na zaman babban cikas ga ƙoƙarin ƙulla wata sabuwar dangantakar cinikaiya a taron kolin kungiyar EU da ta AU na farko cikin shekaru bakwai. Shugaban ƙasar Senegal Abdoulaye Wade ya yi watsi da matsin lambar da birnin Brussels ke yi na ƙulla sabbin yarjeniyoyin ciniki da kasashen Afirka kafin ranar 31 ga watannan na desamba.