Shugabannin Ƙungiyar EU sun yi kira ga gwamnatin Sudan da ta amince da girke dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin Darfur. | Labarai | DW | 15.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin Ƙungiyar EU sun yi kira ga gwamnatin Sudan da ta amince da girke dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin Darfur.

A taron ƙolin da suke yi a birnin Brussels, shugabannin ƙungiyar Haɗin Kan Turai, sun yi kira ga gwamnatin Sudan da ta ɗau matakan gaggawa, wajen amincewa da girke dakaraun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin Darfur. A cikin wata sanarwar da suka bayar yau a gun taron nasu, shugabannin sun bayyana damuwarsu ga haɓakar tashe-tashen hankullan da ake ta samu a yankin. Kawo yanzu dai, mahukuntan birnin Khartoum na watsi ne da batun girke dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniyar. Kazalika kuma, sun ce ba za su yi amanna da shawarar girke dakarun haɗin gwiwa na Ƙungiyar Tarayyar Afirka da na Majalisar Ɗinkin Duniyar ba.