Shugabannin ƙungiyar APEC sun buɗe taron ƙolinsu a Sydney | Labarai | DW | 08.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin ƙungiyar APEC sun buɗe taron ƙolinsu a Sydney

An bude taron kolin kungiyar kasashen gamaiyar tattalin arzikin Asiya da Pacifik wato APEC a birnin Sydney na kasar Australiya a karkashin tsauraran matakan tsaro. Shugabannin kasashe 21 na kungiyar ciki har da shugaban Amirka GWB da shugaban China Hu Jintao da shugaba Valdimir Putin na Rasha na daga cikin shugabanin da ake halarta taron a birnin na Sydney. Muhimman batutuwan da shugabannin ke mayar da hankali kan su sun hada da kare muhalli da na huldar ciniki a duniya. Dubban masu zanga-zanga suka hallara a tsakiyar birnin Sydney don nuna adawa da shugaba Bush da yakin Iraqi da kuma rashin yin wata hobbasa daga bangaren shugabannin siyasa don kare muhalli.