Shugabannin ƙasashen Ƙungiyar ECOWAS sun ba da shawarar tsawaita wa’adin shugaba Gbagbo na Côte d’Ivoire da shekara ɗaya. | Labarai | DW | 09.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin ƙasashen Ƙungiyar ECOWAS sun ba da shawarar tsawaita wa’adin shugaba Gbagbo na Côte d’Ivoire da shekara ɗaya.

Shugabannin ƙasashen ECOWAS, wato ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, waɗanda suka yi wani taro a ƙarshen mako a birnin Abujan Najeriya, don tattauna batun ƙasar Côte d’Ivoire, sun ba da shawarar tsawaita wa’adin shugaban ƙasar Laurent Gbagbo har zuwa shekara ɗaya kuma. Wata sanarwar da aka buga yau a birnin Monroviya na ƙasar Laberiya, wadda ita ce ke jagonrancin ƙungiyar a halin yanzu, ta ce shugabannin za su bar Majalisar Ɗinkin Duniya ne ta yanke shawara kan yadda ababa za su kasance nan gaba a Côte d’Ivoire ɗin, bayan farkon wa’adin shugaba Gbagbon ya cika a ƙarshen wannan watan.

A shekarar bara ma sai da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tsawaita wa’adin shugaba Gbagbon da shekara ɗaya, don bai wa ƙasar damar tsara shirye-shiryen zaɓe a ƙarshen watan Oktoba na wannan shekarar. Amma kawo yanzu, babu abin da aka taɓuka wajen cim ma wannan burin. Matsalolin da suka hana ruwa gudu wajen aiwatad da shirye-shiryen dai sun haɗa ne da gazawar da aka yi wajen kwance wa abokan hamayyar ƙasar ɗamara da kuma cikas da aka samu wajen rajistan dubban masu zaɓe da ba su da cikakkun takardun shaidar asalinsu.