shugabanin Israila da Palasdinu aun amince ganawa akai akai | Labarai | DW | 27.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

shugabanin Israila da Palasdinu aun amince ganawa akai akai

Shugabanin Israila da na Palasdinwa sun amince su rika ganawa bayan kowane sati biyu haka kuma zasu tattauna matakan farko da zasu kai ga kafa kasar Palasdinu mai cin gashin kanta.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta sanar da haka lokacin ziyararta a yankin.

Rice ta kuma roki kasashen larabawa da su mika hannun kawance ga Israilan,bayan sun maince da sake farfado da shirin zaman lafiya da yawi Israila tayin kafa hulda tsakani muddin dai ta janye gabaki daya daga yankuna data mamaye bayan yakin 1967.