Shugabanin duniya na yin Allah wadai da harin bom a Lebanon | Labarai | DW | 20.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabanin duniya na yin Allah wadai da harin bom a Lebanon

Shugabanin ƙasashen duniya na cigaba da yin Allah wadai da harin bom ɗin da aka yi a Lebanon wanda ya hallaka wani ɗan Majalisar dokoki Antoine Ghanem tare da mukarraban sa bakwai. A ranar laraba data wuce ne a birnin Beirut aka yiwa ɗan majalisar kisan gilla, yayin da yake wucewa a motar sa, harin da yan jamíyar sa ta mabiya addinin Kirista suka ɗora alhakin sa ga mahukuta a Damascus. Syrian dai ita ma ta yi tur da Allah wadai da harin. Harin ya zo ne ƙasa da mako guda kafin majalisar dokokin ta gudanar da zaɓen sabon shugaban ƙasa. Antoine Ghanem shi ne mutum na bakwai a jerin manyan yan siyasar Lebanon waɗanda ke adawa da Siyaria da aka yiwa kisan gilla, tun bayan kisan da aka yiwa tsohon P/M ƙasar Rafik al-Hariri a shekarar 2005. Shugaban Amurka George W Bush ya yi kakkausar suka da harin wanda yace aiki ne na marasa imani. Yana mai jaddada goyon bayan Washington ga alúmar Lebanon na tauye dukkan wani yunƙuri na ƙasashen Syria da Iran domin wargaza Lebanon.