Shugabancin Kasar Netherlands Ga Kungiyar Tarayyar Turai | Siyasa | DW | 21.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugabancin Kasar Netherlands Ga Kungiyar Tarayyar Turai

A yau laraba ne P/M kasar Netherlands Jan-Peter Balkanende ya gabatar da jawabi a game da manufofinsa ga majalisar Turai dake Strassburg

Babban abin da ya fi ci wa P/M kasar Netherlands Jan-Peter Balkenende tuwo a kwarya shi ne sakamakon zaben majalisar Turai watan yunin da ya gabata. Domin kuwa sakamakon zaben yana mai bayyanarwa ne a fili yadda jama’a ke dari-dari da manufar hadin kan Turai, musamman ma a sabbin kasashen gabaci da na tsakiyar nahiyar da aka karba a Kungiyar Tarayyar Turai a farkon watan mayun da ya gabata. Dangane da haka P/M na kasar Netherlands dake shugabancin kungiyar yake neman aiki kafada-da-kafada da majalisar Turai. Ya ce babu wani dalili na karayar zuci. A maimakon haka wajibi ne a tashi tsaye wajen wayar da jama’a a game da alkiblar da aka fuskanta da kuma muhimmancin hadin kan Turai domin tinkarar matsalolin nahiyar baki dayanta. Daftarin tsarin mulki bai daya da aka zayyana ka iya zama wata madogara ta samun ci gaba a wannan manufa. A cikin jawabinsa ga wakilan majalisar Turai Jan-Peter Balkenende ya sha nanata yin kiran karfafa hadin kai ta yadda kome zai tafi salin alin dangane da kasashen da za a karba nan gaba a KTT. A cikin watan desimba mai zuwa ne shuagabannin kasashen kungiyar zasu tsayar da shawara a game da ranar da za a fara shawarwarin karbar kasar Turkiyya. Wajibi ne a kamanta adalci wajen kimanta ci gaban da kasar ta Turkiyya ta samu akan hanyar neman karbarta a kungiyar ta tarayyar Turai. Bai kamata a nemi garkama mata wasu sabbin sharudda domin hana ruwa gudu akan wannan manufa ba, in ji P/M kasar Netherlands, wanda ya kara da cewar:

Ka da mu bari fargaba game da musulunci ta kawar da mu daga hanya madaidaiciya. Adawa da addini bata da nasaba da akidar Kungiyar Tarayyar Turai. Mutanen da ya kamata a tinkaresu su ne wadanda ke amfani da addini domin neman ta da zaune tsaye.

A nasa bangaren kakakin ‘yan Socialist a majalisar Turai Martin Schulz dan jam’iyyar SPD ya goyi bayan wannan lafazi na Balkenende, inda ya ce yau tsawon shekaru 40 ke nan nahiyar Turai na shafa wa kasar Turkiyya zuma a baki, kuma a saboda haka bai kamata a yanzun a nemi bijire mata ba. Babu wata matsala a game da Musulunci. Kasar Turkiyya na danganta manufofinta da walwala da ‘yanci da hadin kai da kuma ‘yan-uwantaka, wanda yayi daidai da manufofin kasashen yammaci. Amma bisa ga ra’ayin wakilin jam’iyyar CDU Hans-Gert Pöttering, bai kamata a ba wa Turkiyya damar shigowa KTT ba, a maimakon haka a yi mata tayin kawance na musamman. Shi kuwa shugaban hukumar zartaswa ta kungiyar Romano Prodi kira yayi da a bude kofofin kungiyar tarayyar Turai domin karbar kasashen yankin Balkan. A cikin jawabinsa ga majalisar ta Turai a Strassburg P/M kasar Netherlands Jan-Peter Bakenende ya tabo maganar kudi mai sarkakiyar gaske, inda ya ce kasarsa zata yi bakin kokarinta wajen cimma daidaituwa a game da bunkasa yawan kasafin kudin hukumar zartaswa ta kungiyar da misalin kashi daya da rara cikin dari har tsawon shekaru bakwai masu zuwa.