1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabancin Jamus ga Kungiyar Tarayyar Turai

December 14, 2006

A yau alhamis shugabar gwamnati Angela Merkel ta gabatar da bayani akan manufofin gwamnatinta dangane da shugabancin Jamus ga KTT

https://p.dw.com/p/Btx3
Angela Merkel
Angela MerkelHoto: AP

“Tare da hadin kai nahiyar Turai zata cimma nasara”. A karkashin wannan taken ne Jamus ke fatan tafiyar da shugabancinta ga Kungiyar Tarayyar Turai tun daga daya ga watan janairu mai kamawa. Ita kuma shugabar gwamnati Angela Merkel ta dauri cikakkiyar niyyar daukar wannan nauyi, inda ta ce zata gabatar da wani shirin aiki dangane da manufofin makamashi na kasashen Turai tare da sassauta dangantakar ciniki akan wutar lantarki da gas tsakanin kasashen. Kazalika zata ba da cikakken goyan baya ga manufar kare makomar yanayi tare da sake farfado da shawarwarin daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen KTT. Bugu da kari kuma shugabar gwamnatin ta Jamus ta lashi takobin yin bakin kokarinta wajen karfafa matsayin kungiyar a fannin tattalin arziki. Merkel ta kara da cewar:

“Muddin ba a da kakkarfan tattalin arziki kuma mutane ba su da tabbas game da makomar rayuwarsu to kuwa kungiyar tarayyar Turai ba zata iya yin katabus a dangantakar ketare ba. Hakan na ma’anar samun kyakkyawan ci gaba a Brussels tare da karfafa hadin kan kasashen kungiyar baki daya. Manufofin KTT zasu zama masu tasiri ne idan an cimma nasarar kayyade yawan marasa aikin yi su kuma kamfanonin kasashen suka samu haske game da makomarsu. Hakan kuwa na nufin kara karfafa hadin kan manufofi na cikin gida da na ketare ne tsakanin illahirin kasashen KTT.”

Muhimmin abu dangane da manufofi na ketare dai shi ne kasashen kungiyar su rika magana da murya guda, domin kuwa rarrabuwar kawunansu zai raunana matsayinta, musamman ma idan an yi batu game da shawarwarin sasanta rikicin YGTTs da dangantakar ciniki ta kasa da kasa. Angela Merkel ta kara da yin kira ga wakilan majalisar dokoki ta Bundestag da su yi amfani da damar da shugabancin Jamus ga KTT zata ba su bisa manufa. A nasu bangaren ‘yan hamayya a shirye suke su bai wa gwamnati hadin kai saboda shugabancin KTT wata mashala ce ta kasa baki daya. To sai dai kuma duk da haka sai da aka fuskanci wasu ‘ya soke-soke akan manufofin gwamnati. Renate Künast wakiliyar The Greens ta ce gwamnati kame-kame take yi bata da wani takamaiman shiri:

“Jamus na bukatar sani daga gareki ko shin wace alkibla kika fuskanta. Shin wadanne matakai zaki dauka kuma da su wane ne zaki yi hadin kai domin cimma manufofin da kika sa gaba. Abu daya da zan fada miki uwargida Merkel shi ne: A jawabin da kika bayar ba mu ji kin ambaci wasu takamaimun manufofi ba. Duka-duka maganganu ne da ba su da tushe.”

Wannan dai shi ne karo na fartko da Jamus zata ja akalar shugabancin kungiyar tarayyar Turai tun abin da ya kama daga shekara ta 1999.