1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Zambiya ya suma a lokacin biki

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 8, 2015

Ana tsaka da bikin ranar mata ne shugaba Edgar Lungu ya suma. Fadar shugaban kasa ta ce ya na fama da zazzaɓin ciwon sauro. 'Yan adawa suka ce ciwon sugar ne.

https://p.dw.com/p/1EnQf
Sambia Lusaka Präsidentschaftswahlen Edgar Lungu
Hoto: REUTERS/R. Ward

Shugaban ƙasar Zambiya Edgar Lungu ya yanke jiki ya faɗi a lokacin da ya ke halartar bikin ranar kare 'yanci mata da ya gudana a Lusaka babban birnin kasar. An dai garzaya da shi asibitin soji cikin gaggawa domin bashi kulawa da ta dace. sai dai kuma cikin wata sanarwa da ta fitar, fadar shugaban kasa ta yi kira ga al'umma da suka kwatar da hankulansu, saboda gajiya ce kawai ke damun shugaban da kuma zazzabin cizon sauro.

Sai dai kuma 'yan adawa na zargin shugaba Lungu da marar ciwon sukari watau Diabetis. Shugaban na Zambiya mai shekaru 58 a duniya ya dare kan juerar mulki ne watannin biyun da suka gabata bayan rasuwar Micheal Sata a lokacin da ya ke tsaka da wa'adinsa na mulki. Marigya Michael sata ya zama shugaba na biyu da ya mutu a cikin shekaru shida a kan karagar mulki. 'yan siyasar kasar da dama sun ta nema a fara duba lafiyar kowani dan takara kafin a bashi damar shiga a dama d shi a zabe, amma kuma hakarsu ta kasa cimma ruwa.