Shugaban yan adawa na Zimbabwe ya baiyana gaban kotu | Labarai | DW | 13.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban yan adawa na Zimbabwe ya baiyana gaban kotu

Shugaban yan adawa na kasar Zimbabwe Morgan Tsvangirai da wasu yan adawa da dama sun baiyana a gaban kotu bayan tsare su da akayi a karshen mako.

Magoya bayansu sunce tsvangirai da sauran magoya bayansa akwai alamun sun sha kashi a hannun jamian tsaro saboda yadda suka fito jikinsu duk a daddauje.

Tsare su da akayi ya janyo suka ga shugaba Mugabe da gwamnatinsa.

Lauyoyi dai sunce yan sanda sunki basu izni kaiwa ga wadannan mutane duk kuwa da umurni da wani alkali ya bayar.

A ranar lahadin dai yan sanda sun harbe wani mutum a lokacinda rikici ya barke wajen wani gangami da yan adawa suka kira suna masu jan hankalin gwamnati data bada damar tataunawa game da siyasa da tattalin arzikin kasar.