Shugaban Venezuela ya bayyana Bush da cewa ya fi kama da Hitler | Labarai | DW | 05.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Venezuela ya bayyana Bush da cewa ya fi kama da Hitler

Shugaban Venezuela Hugo Chavez ya sake bayyana Amirka da cewa babbar barazana ce ga kasarsa. Shugaban ya kuma ba da sanarwar sayen bindigogi masu saraffa kansu har miliyan daya a wani mataki na kasancewa cikin shirin ko-takwana. Shugaba Chavez ya fadawa dubban magoya bayansa a birnin Caracas cewa rashin sanin halin ya kamata na shugaban Amirka GWB bai da iyaka. A lokacin da yake mayar da martani ga kalaman da sakataren tsaron Amirka Donald Rumsfeld yayi inda ya kwatanta shugaba Chavez da Hitler, shugaban na Venezuela ya ce ai a duniyar nan ba wanda ya fi Bush yin kama da Hitler. A kwanakin nan dai danganta tsakanin Venezuela da Amirka ta kara rincabewa bayan da suka kori jami´an diplomasiyar su.