1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan ya zargi Tarayyar Turai da taimakon ta'addanci

November 6, 2016

Ya ce 'yan kasashen yamma masu sukar lamiri kada su tsoma baki a cikin abin da bai shafe su ba. Kuma Bai damu ba idan sun kira shi dan kama karya, ko wani abu daban.

https://p.dw.com/p/2SFDp
Türkei Recep Tayyip Erdogan
Hoto: picture alliance /dpa/S. Suna

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya zargi tarayyar Turai da taimakawa ta'addanci ta hanyar goyon bayan kungiyar Kurdawa ta PKK. Ya ce bai damu da abin da Tarayyar Turai za ta fada a kansa ba ko za ta kira shi mai mulkin kama karya ne, yayin da yake ci gaba da yin dirar mikiya a kan Kurdawa 'yan fafutuka da masu goya musu baya.

Kasar Turkiyar dai ta fuskanci kakkausar suka daga kasashen duniya sakamakon kama shugabanin jam'iyyar adawa ta Kurdawa HDP tare da wasu 'yan majalisar dokokin Jam'iyyar. Gwamnatin ta na zargin jam'iyyar ta HDP da alaka da kungiyar PKK, zargin kuma da jam'iyyar ta musanta.